Tasirin Daidaita Rubutu ga Al’umma: Tsokaci daga harshen Hausa

Authors

  • S. Garba Sashen Harsuna da Al’adun Afirka Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya Author
  • H. M. Bugaje Sashen Harsuna da Al’adun Afirka Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya Author

Keywords:

Daidaita rubutu, Harshen Hausa.

Abstract

Sanannen abu ne cewa harshe shi ne mafi girman ni’imar da Ubangiji ya yi wa
ɗan’adam baiwa da ita don kyautata rayuwarsu da kyautata fahimtar junansu.
Wannan kuma shi ne sinadarin more rayuwar ɗan’adam da ci gabansa da
bunƙasarsa ta kowace fuska ta rayuwa. Rubutu kuwa hanya ce ta isar da saƙo cikin
alamu musamman zuwa ga wanda yake nesa. Watau wanda wurin rayuwarsu ko
zamanin rayuwarsu ya bambanta. Sannan kuma ga shi ana buƙatar rubutu ya iya
wakiltar murya wacce kuma take cancanzawa daga wani lafazi ko yanayi zuwa
wani. Bugu da ƙari kuma shi rubutu ba a iya maimaita shi don inganta fahimtar
wanda aka yi wa saboda tazarar da ke tsakaninsu. Don haka dole ne a samar da
wani daidaitaccen salo na baiɗaya wanda zai iya wakiltar kowace murya a kowane
yanayi kuma ya sauƙaƙe hanyar hulɗa a tsakanin al’umma. Shi kuwa daidaitaccen
rubutu, shi ne salon rubutun da aka yi tanajin ƙa’idoji da dokokin da za a sarrafa
harshe da su. Daidaita rubutu shi ne yake bayar da damar iya bincike da rubucerubuce a cikin harshen al’umma, sannan kuma a iya koyo da koyar da shi.
Waɗannan abubuwa da aka ambata game da harshe su ne ginshiƙan haɓaka da
bunƙasar kowane harshe na duniya da kuma ci gaban al’umma ta kowace fuska.
Wannan dalili ne ya sanya wannan maƙala ƙoƙarin zaƙulo ire-iren waɗannan
fa’idoji, musamman ga harshen Hausa da al’ummar Hausawa domin jawo
hankalin al’ummar Hausawa game da ƙara kula da tsare wannan muhimmin aiki
ga harshen Hausa. Sannan kuma maƙalar ta faɗakar da Hausawa dangane da
sakaci ko watsi da irin wannan muhimmin aiki da kuma zaƙulo irin haɗarin da ke
tattare da haka.

Downloads

Published

2026-06-26

Issue

Section

Articles